Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewa a jiya Litinin duban al'ummar musulmi mabiyar mazhabar shi'a ne suka gudanar da zanga-zanga a biranan Zariya da Abuja, inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta bi umarni kotu ta kuma saki sheikh Zakzaky domin a fitar da shi kasashen waje a duba lafiyarsa,
Kafin hakan dai a jiya lahadi, an gudanar da irin wannan zanga-zanga a birane da dama na kasar ciki kuwa har da birnin kaduna, inda jami'an 'yan kasar suka kashe mutum guda daga cikin mahalarta zanga-zangar.
Zanga-zangar dai ta biyo bayan wasu labarai ne da suke nuna cewa, jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya din Sheikh Ibrahim El-Zakzaky yana cikin mawuyacin hali na rashin lafiya, a inda ake tsare shi, da yake bukatar kula ta likitoci na gaggawa. Don haka masu zanga-zangar suka kira gwamnatin Muhammadu Buhari da ta gaggauta sako shi don fita da shi wajen kasar don sama masa kula ta musamman cikin gaggawa.